fidelitybank

Mun cafke buhun Tabar Wiwi 532 a gaɓar ruwa ta Tincan dake Legas – NDLEA

Date:

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce, ta kama buhuna guda 532, wani nau’in tabar wiwi mai suna Sativa (Hemp Indiya) a tashar jirgin ruwa na Tincan, dake jihar Legas.

Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar Mista Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Babafemi ya ce, an gano magungunan masu nauyin kilogiram 265.25 a cikin wata bakar bas din Toyota Sienna, a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta.

Ya ce motar bas din daya ce daga cikin motoci uku da ke cikin akwati mai lamba MSMU 6029570 da ta fito daga birnin Montreal na kasar Canada.

“An kama su ne a lokacin jarrabawar hadin gwiwa 100 bisa 100 da jami’an hukumar kwastam da sauran masu ruwa da tsaki.

“Washegari, Alhamis, jami’an sun sake yin wani kama wasu fakiti 75 na nau’in abu iri ɗaya mai nauyin 37.5kg a cikin akwati mai lamba FSCU-9274613, wanda ya fito daga Kanada,” in ji shi.

A wani labarin kuma, A Adamawa, jami’an NDLEA a ranar Alhamis tare da goyon bayan jami’an rundunar ‘yan sandan farin kaya ta 3, Mayo Belwa, sun tsare wani mutum mai suna Joseph Peter dan shekaru 49 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Babafemi ya ce, an samu wanda ake zargin dauke da bulo na tabar wiwi guda 425 masu nauyin nauyin kilogiram 291.200 a cikin motarsa ​​kirar Toyota Camry mai lamba Lagos KSF 381 HM.

Kakakin hukumar ta NDLEA ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya fito da kayan ne daga Edo domin a kai shi a Yola, Adamawa.

Haka kuma an kama wasu mutane biyu: Adekunle Adebayo mai shekaru 50 da kuma Yahaya Mamuda mai shekaru 35 tare da tsare su a unguwar Gadar Tamburawa da ke Kano a ranar Talata da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 29.5.

Babafemi ya ce jami’an NDLEA a Legas sun kuma gano kilogiram 1,169 na nau’in sinadari iri daya da aka boye a cikin wata motar bas da ke kan titin Orchard, Ajah, ranar Lahadi 4 ga watan Agusta.

A cewarsa, an lalatar da tabar wiwi kasa da ya kai kilogiram 1,230.00 a kadada uku na gonaki a dajin Ikeje, kauyen Edimogo, karamar hukumar Igalamela/ Odolu, Kogi ranar Juma’a.

“Jami’an NDLEA da ke samun goyon bayan sojojin Najeriya ne suka yi hakan yayin da ake tsare da mai shi, Danjuma Maji, mai shekaru 40,” in ji shi.

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp