fidelitybank

Mun buɗe wuraren da aka ɓoye abinci a Kano – Muhyi

Date:

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano, ta ce ta buɗe manya-manyan wuraren ajiya da ta kulle a baya bisa zargin an ɓoye kayan abinci.

Hukumar ta ce ta tattauna da masu wuraren inda suka cimma matsaya a kan yadda farashi zai sauka.

A ƙarshen mako ne hukumar ta a’Anti-corruption’ ta kai samame manyan rumbunan ajiye kayan abinci da ake zargin an boye kayan abinci a sassan jihar Kano bayan ƙorafe-ƙorafen da suka ce sun karɓa daga jama’a.

Shugaban hukumar Muhyi magaji Rimin Gado, yace bayan sun garƙame rumbunan ajiye kayan abinci a wurare daban-daban ciki har da kasuwar Dawanau a Kano, masu wuraren sun kai kansu hukumar inda suka zauna tare da cimma matsaya.

Kawo yanzu dai an buɗe manyan rumbunan ajiya da dama bayan zaman da aka yi.

Shugabannin kasuwannin jihar sun tabbatar wa da BBC buɗe manyan rumbunan ajiyar.

Shugaban hukumar anti-corruption mai yaki da cin hanci a Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado yace ko yanzu sun cimma manufarsu kasancewar farashin ya fara sauka.

Muhuyi Rimin Gado ya ƙara da cewa akwai sito-sito waɗanda suke maƙare da kayan abincin tallafi, sun kuma kyalesu bayan binciken da suka yi, ya tabbatar da cewa ba boye kayan aka yi ba, don a ci ƙazamar riba.

Yayin da ‘yan ƙasa ke ci gaba da kiraye-kirayen a sassauta irin tsananin da ake fama da shi, hukumomi a matakai daban-daban na iƙirarin cewa suna iyakar ƙoƙarinsu wajen kyautata halin da ake ciki, amma masu nazari na cewa ya kamata gwamnati ta gaggauta shawo kan matsalar tun kafin al’amarin ya kazance.

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp