fidelitybank

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Date:

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin ranar jimami a jihar, inda ya amince da ba ma’aikatan jihar hutun aiki domin alhinin waɗanda suka rasu daga cikin tawagar ƴanwasanta da suke yi hatsari a hanyarsu ta komawa gida daga wasannin ƙasa da aka yi a Ogun.

Zuwa yanzu dai inda mutum 22 suka rasu daga cikin tawagar ƴanwasan, sannan wasu kuma suka jikkata.

A sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya kaɗu matuƙa da samun labarin mutuwar ƴanwasan, lamarin da ya bayyana da yanayi mai ɗaga hankali da damuwa.

“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, muna miƙa ta’aziyarmu ga iyaye da iyali da ƴanuwan waɗanda suka rasu. Sanan ina kira ga dukkan musulmi a jihar da su yi addu’ar samun rahamar Allah ga waɗanda suka rasu.”

Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen kula da waɗanda suka jikkata, da kuma tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu.

vgn news 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp