Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’Adama mai suna Progressive Mind for Developement Initiative, ta bankado yadda wasu masu hannu da shuni sukan tura wakilansu zuwa gonaki, suna saye kayan amfanin gona, tun kafin a kai ga yin girbi.
Haka kuma ƙungiyar ta yi zargin cewar bayan sun saye kayan amfanin sai su boye su, har sai farashinsu ya yi tsada matuka, sannan su futo da shi su sayar.
Ƙungiyar ta ce ta gudanar da binciken nata ne a jihohi biyar na Najeriya, da suka haɗa da jihohin Adamawa, da Benuwai, da Kaduna, da Kano, sai Taraba.
Kwamret Abubakar AbdusSalam, shi ne shugaban ƙungiyar, ya ya ce “ ganin cewar irin wahalhalun da alumma ke fama da su na yunwa da ƙarancin abinci, da ƙarancin kudi da stadar rayuwa, a ƙoƙarin mu na tabbatar da ina aka sami wanna mastala, muka gano cewar akwai masu hannu da shuni da ke shiga har cikin ƙauyuka, su sami manomi har gonarsa, su ɗauki rabin kuɗin aikin gonar su ba su.