Babbar kungiyar kiwon lafiya da ke bayar da lasisi ta jajirce cewa rijistar likitoci a Birtaniya ta bada lasisi ga likitoci ‘yan Najeriya 266 a watan Yuni da Yuli na 2022, a cewar rahoton jaridar Punch.
Tasirin haka shi ne akalla likitoci ‘yan Najeriya uku ake bai wa lasisi a kowace rana duk da yunkurin gamnati na dakile ficewar likitoci da jami’an kiwon lafiya daga kasar.
A halin yanzu akwai likitoci da suka samu horo a Najeriya 9,976 da ke aiki a Birtaniya.
Wannan adadi bai kunshi wasu likitoci ba wadanda ‘yan Najeriya ne amma ba su samu horo a Najeriyar ba, a cewar rahoton.
Yanzu haka Najeriya ce kasa ta uku da ta fi kowace yawan likitoci da ke aiki a Birtaniya – bayan Indiya da Pakistan.
Sai dai duk da haka kasar na fama da karancin likitoci.
Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce, akwai likitoci 100,000 da suka yi rijista da ita.


