Kungiyar Malaman Jami’o’I ta ASUU, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga Gwamnatin Tarayya, da ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar a shekarar 2009, ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban kungiyar ASUU reshen Uyo, Farfesa Opeyemi Olajide, ya ce, a shekarar 2022 jami’o’in gwamnati sun shiga yajin aikin watanni 8 kan matsalolin da suka addabe su.
Ya bayyana takaicinsa cewa bayan shekaru biyu, Gwamnatin Tarayya ba ta son mutunta yarjejeniyar da kuma biyan bukatunsu.
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa, kungiyar ta tuntubi hukumomin da abin ya shafa, domin su shiga tsakani tare da sanya gwamnati ta yi abin da ya dace, domin dakile duk wani cikas ga harkokin ilimi, amma, babu wani sakamako mai kyau inda ta jaddada cewa idan bayan makonni biyu ba a yi komai ba, kungiyar za ta tsayar da aikin ta tare da rufe jami’o’i.