Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Ƙasa, ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu ta fara aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a baya.
Wa’adin na zuwa ne bayan kammala taron shugabannin ƙungiyar na kwana uku da suka gudanar a babban asibitin tarayya da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun.
Gidan Talbijin na Channels TV a Najeriya ya ruwaito cewa likitocin na buƙatar kashi 15 cikin 100 na ƙasafin kuɗin ƙasar ya riƙa tafiya a fannin lafiyar ƙasar, a maimakon kashi 5.7 da a yanzu kasafin kuɗin ke ware wa ɓangaren lafiyar ƙasar.
ƙungiyar likitocin ta ce hakan ne kawai zai magance ɗinbim matsalolijn da suka yi wa fannin lafiyar ƙasar kaka-gida, kamar rashin ɗaukar ma’aikatan da za su cike giɓin da ake da shi a fannin lafiyar.
Haka kuma ƙungiyar na buƙatar yin gyara a fasalin albashin ma’aikatanta cikin gaggawa ta yadda za su samu ƙarin kashi 200 kan albashin likitocin na yanzu.
Kungiyar likitocin kuma na so a gaggauta fara biyan mambobinta albashinsu da a baya aka riƙe musu tun 2014 da 2015 da kuma 2016