Ƙungiyar ɗaliban Najeriya (NANS), ta ba gwamnati wa’adin mako biyu ta ceto ɗaliban koyan aikin likita 20 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue.
Ɗaliban da suka ƙunshi ƴan jihar Borno, da jihar Filato, na kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Ogun domin halartar wani taro.
Muhammad Sabo, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriyar, ya shaida wa BBC cewa “An yi irin wannan abu ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, shi ya sa a wannan karo ba za mu bayar da ƙofa yadda za a cutar da ɗalibanmu ba.”
Ya bayyana cewa shi ya sa ƙungiyar ta ɗeba wa gwamnati wa’adi domin ganin ta yi duk abin da ya kamata domin kuɓutar da ɗaliban.
Ya ƙara da cewa “saɓanin hakan zai sa a ga fushinmu fiye da yadda aka saba gani.”
Ya kuma nuna takaici kan yadda makarantun Najeriya da dama ke fama da matsalar tsaro, wanda hakan ya sanya aka rufe wasu makarantun da dama.