A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da bukatar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ciyo bashin Naira biliyan 10, domin sanya na’urar daukar hoto na CCTV a kan titunan jihar.
Kakakin majalisar Hamisu Ibrahim Chidari ne ya karanta wasikar a zauren majalisar ranar Laraba.
Gwamnan ya bayyana a cikin wasikar cewa, an ba da lamuni ne don bunkasa Optic Cyber da sanya na’urorin daukar hoto na CCTV a dukkan wurare masu mahimmanci a cikin babban birni da shalkwatar masarautu biyar da dai sauransu.
Gwamna Ganduje ya ce, aikin ya zama wajibi ne, saboda ta’azzarar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Ya kara da cewa, jadawalin biyan lamunin ya hada da mai shekaru 10 wanda ya hada da dakatar da watanni 12.