Majalisar Dattawa ta amince da naɗin alkalai 11 na Kotun Koli.
Kwamitin majalisar kan harkokin shari’a da kare hakkin ɗan adam wanda Sanata Tahir Munguno ya jagoranta ne ya tantance dukkan alkalan 11 a ranar Laraba tare da gabatar da rahotonsa gaban ƴan majalisar.
Tun da farko, shugaba Tinubu ne ya aika sunayen alkalan inda ya buƙaci da ta amince da naɗinsu, waɗanda kuma ƙungiyar shari’a ta ƙasa ta bayar da shawarar a naɗa su domin cike guraben alkalan da suka mutu da kuma waɗanda suka ajiye aiki.
Cikin sabbin alkalan da aka amince da naɗinsu akwai mai shari’a Haruna Tsammani, wanda ya jagoranci zaman kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Sauran sun haɗa da mai shari’a Moore Adumein, mai shari’a Jummai Sankey, mai shari’a Chidiebere Uwa, da kuma mai shari’a Chioma Nwosu-Iheme.


