Hukumar Alhazai ta kasa, ta amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajjn bana, kamar yadda kamfanonin jiragen aman da za su yi jigilar alhazan suka nema.
Kwamishinan kuɗi da ma’aikata na hukumar Nura Hassan Yakasai, ne ya tabbatar da haka lokacin wata tattaunawa da BBC, bayan taron da hukumar ta yi a Abuja babban birnin ƙasar.
Ya ce kamfanonin jigilar alhazan ne suka buƙaci hakan saboda yaƙin da ake a Sudan, ya sanya dole sai sun zagaya, ba za su bi ta sararin samaniyar Sudan ba.
Ya ce kamfanonin jiragen sun ce sai sun yi zagaye na ƙarin sa’o’i biyu, kuma a kowacce sa’a kamfanonin sun ce jiragen kan sha mai na kusan miliyan takwas.
A don haka ne hukumar da kamfanonin jiragen suka amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujera.
Haka kuma ya tabbatar da ƙarin kuɗin biza da aka yi na wajen dala 65.
To sai dai ya ce hukumar na tattaunawa da gwamnati domin ganin yadda za a biya ƙarin ƙuɗaɗen.