Wata kungiyar da ta balle daga kawancen jam’iyyu marasa rinjaye, ta bayyana goyon bayanta ga Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin kakakin majalisa da mataimakinsa.
Sabon bangaren karkashin jagorancin Idu Igariwey ya sanar da amincewar Abbas da Kalu a ranar Litinin bayan wani taro da suka yi a Abuja.
Idan dai za a iya tunawa a baya jam’iyyar tsiraru ta bayyana shirin neman wanda zai marawa baya.
Hakan ya biyo bayan rashin samun dan takara daga cikinta da zai kalubalanci jam’iyya mai mulki.
Sai dai yayin da taron ke gudana, bangaren Mista Igariwey ya sanar da daukar Abbas da Kalu.
Sanarwar ta kara da cewa ” Nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, za mu hadu a babban taron ‘yan tsirarun jam’iyyu don tattaunawa tare da tabbatar da amincewar shugaban majalisar da mataimakinsa na majalisar wakilai ta 10,” in ji sanarwar.