fidelitybank

Mun amince a fara yin allurar riga-kafin Maleria – NAFDAC

Date:

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC, ta amince a fara yi wa ‘yan ƙasa allurar riga-kafin zazzaɓin cizon sauro mai suna R21.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, an sanar da ministan lafiya da hukumar bunƙasa lafiya a matakin farko game da wannan mataki na amincewa da riga-kafin don ɗaukar matakan da suka dace na yin allurar ga jama’a

NAFDAC ta kuma buƙaci faɗaɗa gwaje-gwajen da ake yi ta yadda matakan za su ƙunshi nazarin illar da allurar ka iya yi a Najeriya.

Ta ce za a yi amfani da riga-kafin ne wajen hana kamuwa da zazzaɓin maleriya ga ƙananan yara ‘yan wata biyar zuwa ‘yan shekara uku da haihuwa.

Sanarwar ta NAFDAC ta ce, ana samun zazzaɓin cizon sauro a duk faɗin Najeriya, kuma kashi 97% na al’ummar ƙasar ne ke cikin hatsarin kamuwa da maleriya.

A cewar rahoton zazzaɓin cizon sauro na duniya na 2021, Najeriya ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar maleriya. Kashi 27% na masu kamuwa da zazzaɓin cizon sauro a duniya, ana samun su ne a Najeriya.

Kuma ƙasar ce ta fi yawan mutanen da suka mutu sanadin zazzaɓin maleriya a 2020.

Haka zalika, Najeriya ce take da ƙiyasin kashi 55.2% na mutanen da suka kamu da cutar zazzaɓin cizon sauro a Afirka ta Yamma cikin shekara ta 2020.

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp