Wata ƙungiyar masu rajin kishin Islama a Iraƙi ta ce, ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa uku a yankin Tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye da safiyar yau, kamar yadda wata sanarwa da ƙungiyar Hezbollah ta fitar.
Ƙungiyar – wadda ke ƙawance da Hezbollah da sauran ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran – na adawa da Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya.
A wasu lokutan waɗannan ƙungiyoyi na ayyana kansu da ‘Dakarun Turjiya’
Kawo yanzu rundunar sojin Isra’ila ba ta ce komai ba game da rahoton, kuma ba a sani ba ko harin ya yi mata wata ɓarna.