‘Yan bindiga sun kai wani mumunan hari a yankin Karfi da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan ta’addan sun kashe akalla mutum 17, wasu da dama sun jikkata.
Majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun farmaki aƙalla ƙauyuƙa biyar da ke karkashin gundumar Kari, suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.
Majiyar tace: “Yan bindiga sun shigo da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Jumu’a, suka buɗe wuta kan mazauna kauyukan kan mai uwa da wabi, sun kashe mutane 17 kuma sun saci kayyakin mutanen da basu ji ba su gani ba.”
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar a majalisar dokokin jihar Katsina, Aminu Ibrahim Saidu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce,“Tuni na kai ziyara ƙauyukan da lamarin ya shafa, domin yi wa iyalan waɗan da lamarin ya shafa ta’aziyya da jajanta musu”. A cewar Aminu.