Mummunan farin da ba a taba gani ba cikin shekara 40 na ci gaba da mamaye gabashin Afirka
Hukumar kula da abinci ta duniya ta ce zuwa karshen shekarar da muke cikin, kusan mutum miliyan 20 ne ke fuskantar barazanar fadawa cikin kangin yunwa sakamakon mummunan fari a kasashen Kenya, da Habasha, da kuma Somaliya.
Somali ya ce, inda matsalar ta fi kamari inda kusan rabin al’umar kasar ke cikin wanna hali, inda daruruwan mutane ke barin gidajensu, domi komawa sansanin ‘yan gudun hijira.
Dubban yara na gararamba a sansanonin ‘yan gudun hijira, yayin da iyayensu ke shiga manyan biranen kasar domin nemo mu su abin da za su ci.
Haka kuma ana ci gaba da samun rahotonnin karuwar mace-macen kananan yara a asibitocin kasar saboda matsalar karancin abinci. a cewar BBC.