Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu riƙe da madafun iko a gwamnatinsa.
A lokacin taron majalisar zartarwar jihar, Abba gida-gida ya buƙaci mambobin majalisar zartarwarsa su yi aiki bisa ƙwarewa da mutunta aikinsu.
Gargaɗin na zuwa ne bayan ritayar kwamishinan sufuri na jihar, Ibrahim Namadi kan zarginsa da hannu a belin Danwawu, mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.
“Bari na gaya muku gaskiya, ba za mu lamunci duk wata ɗabi’ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba, don haka dole kowane mai riƙe da muƙami ya lura da kyau kan abubuwan da zai yi,” in ji shi.
Gwamnan ya ce, masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa ba ofishinsu kawai suke wakilita ba, suna wakiltar duka gwamnatin ne.
”Mun zo gwamnati ne da nufin tsaftace tarbiyya da inganta rayuwar al’ummar Kano, don haka ba za mu sauka daga kan layi ba”, kamar yadda ya bayyana.