fidelitybank

Muhuyi ya shigar da kara ya na kalubantar tsige shi da gwamnati Kano ta yi

Date:

Shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya shigar da kara a gaban kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja, ya na kalubalantar tsige shi da gwamnatin Ganduje ta yi a Kano.

A karar da Magaji ya shigar, gwamnatin jihar Kano ce tun a farko da ake tuhuma, yayin da aka saka sunayen manyan Lauyan jihar da majalisar dokokin jihar Kano da Akanta-Janar na jihar Kano da Barista Mahmud Balarabe da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano a matsayin wadanda ake tuhuma na 2, 3, 4, 5 da 6, bi da bi.

Ya na rokon kotu da ta tantance ko ta duba da sashe na 8,15(i),(g), da (h), dokar hukumar korafe-korafen Jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta 2008. Cikin 36 na (1) na kundin tsarin mulki kasa na shekara 1999.

Wanda ake kara na 1 zai iya sa wanda ake kara na 3 ya tantance koken wanda ake kara na hudu ta hanyar dakatar da wanda ake kara daga matsayinsa na shugaban hukumar kare kararrakin jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, neman hakkin mai da’awar na sauraron adalci.

Barista Muhuyi Magaji ta bakin lauyoyinsa, karkashin jagorancin Muhammad Ibrahim Tola, ya kuma bukaci kotun masana’antu ta kasa da ta tantance ko ta hanyar sashe na 4 (a), 5, da 6 na dokar hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta 2008.

Wanda ake kara na 5 ya na da hurumin ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban riko na Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, bayan wa’adin watanni 1 ya dakatar da wanda ake tuhuma da wanda ake tuhuma na 1.

Ya roki kotun da ta bayar da sanarwar wanda ake kara na 3 ba shi da damar tantance koken wanda ake kara na 4 ta hanyar dakatar da wanda ake kara ba tare da ya fara jin ta bakin wanda ake kara ba ta hanyar da ya dace na kare kansa.

Idan za a iya tunawa majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Barista Muhyi Magaji a matsayin shugaban hukumar tun a ranar 5 ga watan Yuli, bisa kin karbar jami’in mai mataki na 4 da aka tura ofishin sa, yayin da a ranar 26 ga wata ya ba da shawarar a kore shi, tare da gurfanar da shi, bisa zargin ya kawo takardar jabu ta rashin lafiya, sai dai kusan wata 7 da faruwar al’amarin har ya zuwa yau ba ace ufam ba, walau daga majalisa ko kuma gwamnatin Kano.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp