Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yi hawan Idi a Kano, bayan gabatar da sallar Idi a masallacin Shehu Tijjani da ke binin Kano, sakamakon tashi da aka yi da ruwan sama a birnin.
Sarkin ya isa gidan Shattima kan doki tare da rakiyar ɗimbin magoya baya, inda a nan aka tsara zai gaisa da gwamnan jihar.
Wakilin BBC da je Kano ya ce sarki Muhammadu Sanusi Na biyu fita sallar Idin ne ta duka hanyoyin da sarkin Kano ya saba fita bisa al’ada, sannan kuma ya dawo ta hanyoyin da aka saba.
Sarkin na kan doki, sannan dawakan zage da raƙuma na biye da shi, sai dai babu mahaya kamar yadda aka saba gani a baya.
Bayan ya gaisa da gwamna a gidan Shettima, sarkin ya zarce filin Ƙwaru, inda ya yi wa al’umma jawabi kafin ya shiga gidansa.
Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci sallar Idi a masallacin – wanda gwamnan jihar da sauran mukarraban gwamnati – suka halarta.