Sabon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya kammala zaman fadancin da ya gudanar a fadarsa da ke Ƙofar Kudu.
Da hantsi ne dai sarkin ya fito daga gidansa a kan doki ya tafi fadar waje, inda ya karɓi gaisuwa daga wajen hakimansa da sauran jami’an gwamnatin Kano.
A jiya daddare ne dai sarkin ya koma gidan sarki tare da rakiyar gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, da sauran jami’an gwamnati. Bayan kammala zaman fadancin, Sarki Muhammadu Sanusi ll ya sake hawa dokinsa zuwa cikin gidan sarki.
A ranar Juma’a ne Gwamna Abba Kabir ya miƙa wa Muhammadu Sanusi ll takardar shaidar naɗi a gidan gwamnatin jihar, bayan ya sake naɗa shi a matsayin sarkin Kano ranar Alhamis, jim kaɗan bayan majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun Kano kwaskwarima