Reshen yankin Sahel na ƙungiyar al-Qaeda ya yi iƙirarin ɗaukar alhakin kashe sojojin Nijar 17 cikin wani hari da ‘yan bindigar masu iƙirarin jihadi suka kai a yankin Tillaberi.
Ƙungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta ɗauki alhakin cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Telegram ranar 17 ga watan Agusta.
Ta ce maharan sun yi wa sojojin kwanton-ɓauna tsakanin garuruwan Boni da Torodi da ke kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso a ranar Talata da ta wuce.
Ƙungiyar ta wallafa hotuna huɗu na motoci da makamai da suka sace bayan harin.
Rundunar sojin Nijar ta ce sojojin 17 aka kashe tare da raunata wasu 20, tana mai cewa ta kashe 100 daga cikin maharan yayin da suke ƙoƙarin guduwa.
Sanarwar ta JNIM na zuwa ne yayin da ƙungiyar Ecowas ke cewa tana shirin tura dakarun soja Nijar ɗin don tilasta wa sojojin mulkin ƙasar dawo da mulkin farar hula bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli.