Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa jamiāan tsaron kasar na samun nasara a yakin da suke da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso yamma da kungiyar gwamnonin arewa maso yamma ta shirya a Katsina a yau Litinin.
Tinubu, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilta, ya tabbatar wa āyan kasar nan cewa ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu mafari ne a yayin da gwamnati ke kara yin kokari wajen samar da ingantaccen muhalli ga āyan kasa.
Ya kuma ce rRundunar sojoji daban-daban irin su Operation Hadin Kai da Operation Safe Haven sun cika alkawarin da suka yi wa alāummar kasa ta hanyar kai hare-hare kamar Boko Haram da āyan bindiga da suka dade suna addabar alāumma.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnati na yin kokari matuka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin jamiāan tsaro domin tabbatar da tsarin bai daya a yaki da masu tada kayar baya.Mu