fidelitybank

Mu na neman Mutane 8 ciki harda Farfesa wanda suka kashe mana jami’ai – Sojoji

Date:

Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce, tana neman wasu mutum takwas ruwa a jallo saboda zargin su da hannu a kisan sojoji 17 a yankin Okuama da ke jihar Delta.

Daraktan yaɗa labaran tsaro Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka yi a hedikwatar tsaron da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Shalkwatar tsaron ta fitar da sunayen mutanen takwas ranar Alhamis da suka haɗa da farfesa Ekpekpo Arthur da Andaowei Dennis Bakriri da Akevwru Daniel Omotegbo sai Akata Malawa David da Sinclear Oliki da Clement Ikolo Ogenerukeywe da Reuben Baru sai kuma Igoli Ebi.

Buba ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya a faɗin Najeriya musamman a yankin Neja Delta su taimaka wa sojoji wajen zaƙulo waɗanda aka ayyana ana neman ruwa a jallo.

A ranar 14 ga watan Maris ne wasu ɓata-gari suka afka wa sojojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umomin yankunan Okuoma da Okoloba inda suka kashe su.

A ranar Laraba ne kuma aka yi jana’izar sojojin a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja inda shugaba Bola Tinubu ya halarta tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp