fidelitybank

Mu na neman dan kasar Birtaniya ruwa a jallo bisa yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu – ‘Yan Sanda

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana neman wani Andrew Wynne dan kasar Birtaniya da ake nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Wynne kuma ana kiransa Andrew Povich ko Drew Povey.

Rundunar ta ce ta kaddamar da wani cikakken bincike na musamman kan yadda wasu sojojin hayar kasashen waje suka kulla makarkashiyar kifar da gwamnatin da aka zaba ta dimokradiyya a Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Litinin.

Adejobi ya ce dan Burtaniya ya yi hayar fili ne a Labor House, Abuja, don yin wani kantin sayar da litattafai na ‘Iva Valley Bookshop’ sannan ya kafa ‘STARS of Nations Schools’ a matsayin fakewa da ayyukansa na zagon kasa.

Adejobi ya kuma shaida wa manema labarai cewa shaidun rubuce-rubuce da ikirari sun nuna cewa Wynne ya ba da umarni tare da sanya ido kan yadda zanga-zangar ta watan Agusta ke gudana.

Babban jami’in ‘yan sandan ya kara da cewa, dan kasar waje ya bayar da shawarwarin kudi da kuma yadda ake gudanar da aiki domin samun sauyin tsarin mulkin da bai dace ba a Najeriya.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara gudanar da cikakken bincike kan ayyukan wani dan kasar waje da kuma ‘yan ta’adda masu yin zagon kasa da ke kulla makarkashiyar kawo cikas ga zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya a Najeriya ta hanyar sauya tsarin mulkin da bai dace ba da kuma kitsa tashin hankali a fadin kasar.

“Bayan tattara bayanan sirri da hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro, an kama wasu mutane tara wadanda ake zargi da samun tallafin kudade daga wasu majiyoyin waje domin tada zaune tsaye a kasar.

“Bincike na farko ya nuna cewa sun kitsa tare da ba da gudummawa ga zanga-zangar tarzoma, yada labaran karya, da kuma yin wasu ayyukan da ba su dace ba don haifar da rikici da kuma tabbatar da haramtacciyar makircinsu na hambarar da gwamnatin dimokuradiyya.”

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp