Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya wallafa wani bidiyo da aka ɗauka a kan titunan birnin Kyiv bayan yaɗa jita-jita a kafofin yaɗa labaran Rasha cewa ya gudu daga ƙasar.
“Ga mu nan duka a nan,” a cewarsa kewaye da masu ba shi shawara da firaministansa.
“Muna kare ‘yancin kanmu ne da ƙasarmu, kuma za mu ci gaba da yin hakan.”
An wayi garin yau Juma’a da sojojin Rasha na kunnawa cikin birnin na Kyiv bayan sun shafe tsawon ranar Alhamis suna fafatawa da dakarun Ukraine a kewayensa.