fidelitybank

Mu na murna da kama riƙaƙƙen Ɗan Daba Gundura – Mazauna Unguwar wƊorayi

Date:

Mazauna yankin unguwar Ɗorayi dake ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, na nuna murnar su bisa nasarar kama ƙasurgumin Ɗan Daban nan da ya addaɓe su mai laƙani da Gundura .

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ce, ta kama wani ƙasurgumin ɗandaba da ake nema ruwa a jallo mai suna Inuwa Zakari wanda aka fi sani da Gundura.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kuma samu nasarar kama wasu ɓata-gari 14 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a samamen da suka yi ranakun 25 da 27 ga watan Oktoba.

Kiyawa ya ce ɗandaban ya addabi al’ummar kwaryar birnin Kano saboda irin laifuka da yake aikatawa.

“Ya kuma kasance wanda ya haɗa baki da wasu wajen kai hari kan kwamandan ƴan bijilanti har suka raunata shi ta hanyar cire masa hannu, da kuma lalata motar ƴan sanda a wani lamari na daban,” in ji Kiyawa.

Kakakin ƴan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka na rundunar, inda daga bisani za a tura su zuwa kotu domin su fuskanci hukunci.

Ya ce rundunar ba za ta lamunci ayyukan ƴandaba ba da kuma aikata sauran laifuka a jihar.

Sai dai shugaban tsaron yankin Ɗorayi, Dr Abdullahi Ɗan Fodio, ya shaidawa manema labarai cewa, dama Gundura ya gundure su, kama shi babban abun farin ciki ne a gare su.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp