Gwamnatin Tarayya ta ce, tana yabawa da jajircewar ƴan ƙasar a daidai wannan lokaci da ake fama da matsaloli a sanadiyar gyare-gyaren inganta tattalin arzikin ƙasar da suka ɓullo da su.
Ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasar, Wale Edun ne bayyana hakan a lokacin da yake yi wa kwamitin harkokin kuɗi na Majalisar Dattawa jawabi, kamar yadda tashar talabijin na Channels ta ruwaito.
Ya ce an kusa gama da shan wahalar, domin a cewarsa an fara ganin nasara a gyare-gyaren da aka ɗauko.
“Manyan gyare-gyaren guda biyu su ne farashin man fetur da kuɗaɗen ƙasashen waje sun an fara ganin haske. Ina ganin akwai buƙatar mu yanawa jajircewar ƴan Najeriya bisa abubuwan da suka jure domin samun wannan nasarar.”
A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa sun zauna ne domin sanin ko gyare-gyaren da aka ɗauko suna aiki, ko akasin haka.