Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ta sha alwashin gurfanar da mutanen da ke yada labaran karya da “labarai masu tayar da hankali” a shafukan sada zumunta da nufin haifar da firgici a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.
Hundeyin dai ya na mayar da martani ne dangane da karuwar farfaganda da tsokanar kabilanci a tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta a gabanin zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.
Karanta Wannan: Zan dawo mulki nan ba da jimawa ba a Osun – Oyetola
Ya kuma bayyana cewa ‘yan sanda a jihar sun fara gudanar da bincike a kan al’amura masu alaka da su da nufin gurfanar da wadanda aka samu da laifi a gaban kuliya.
“Hukumar ta fara binciken wannan abin tsoro da nufin kamawa tare da hukunta wadanda aka samu da laifi.
“An yi kira ga mutanen kirki da mazauna jihar da su yi watsi da duk wani nau’i na sakonni, musamman a shafukan sada zumunta da ke nuna labaran karya, karya, da kuma rashin gaskiya da nufin kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar,” in ji Hundeyin.