fidelitybank

Mu na gudanar da bincike a kan yawan ma’aikatan gwamnati – Tinubu

Date:

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya ce, gwamnatinsa na gudanar da gagarumin bincike kan yawan ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Mista Tinubu ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da shugaban Bankin Duniya Mr. Ajay Banga da ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce ”za mu gudanar da gagarumin bincike, tare da nazarin tsarin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya”.

”Ban amince da adadin mutanen da ke kan rajistar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayyara ba, a baya lokacin da nake gwamna na fuskanci irin wannan matsala”.

Tinubu ya ce gwamnatinsa a shirye take don toshe duk wata kafa da kuɗaɗen gwamnati ke zurarewa.

Sanarawar ta ce za a gudanar da binciken ne domin gyara tsarin aikin gwamnati a ƙasar, tare da sauya dabi’un ‘yan ƙasar da kuma wayar da kan jama’a.

Haka kuma shugaban ya ce a yanzu haka gwamnatinsa na gudanar da wani binciken ƙwaƙaf a babban bankin ƙasar CBN.

Makonni bayan rantsar Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele, bisa zargin aikata ba daidai ba.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp