Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya ce kasar sa ta na goyon bayan Rasha kan mamayar da ta ke yi a Ukraine.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, wanda a ciki ministan ke cewa: “Duk yadda yanayin siyasar duniya zai rikice, China da Rasha za su ci gaba da renon dangantakarsu mai matukar muhimmanci.”
Mista Wang ya bayyana China da Rasha a matsayin makwabta kuma makusantan kasashe masu muradu iri daya, ya kuma ce “dangantaka ce ta kut-da-kut wadda kusan babu irinta a duniya.”