Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce umurnin da sojojin Isra’ila suka bai wa Falasɗinawa na ficewa tsakiyar Gaza, babban koma baya ne ga ƙoƙarin ceton rayukan al’ummar yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.
A ranar Lahadi ne Isra’ila ta umarci Falasɗinawa a Deir el-Balah, da su koma kudancin Gaza saboda ayyukan soji.
MDD ta sake nanata gargaɗin da ta yi cewa al’ummar Gaza da dama na mutuwa saboda yunwa kuma suna buƙatar agajin abinci cikin gaggawa yayin da Isra’ila ke ci gaba da taƙaita shigar da kayan agaji.