fidelitybank

Mu na daf da kama wasu gwamnoni biyu da suka wawurI kudi – EFCC

Date:

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce, ta kammala shirye-shiryen kama wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke karewa wadanda ake zargi da ayyukan rashawa, da kuma wasu gurbatattun masu rike da mukaman gwamnati bayan miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, shi ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da Jaridar Daily Trust. 

Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan waɗanda suke shirin kamawa ba da zarar sun suka daga kan mulki.

Shugaban na EFCC ya ce, akwai ma’aikatun gwmanati guda biyu da hukumar ke bincike a kansu a halin yanzu saboda ayyuka da suka saɓa wa ka’ida da suke yi.

A cewarsa, a ɗaya daga cikin ma’aikatun an yi almundahanar kuɗaɗe Na Naira biliyan 4 na wasu kwangiloli kusan 20 da.

Bawa ya ce, “A yanzu haka, muna binciken ma’aikatu biyu da aka biya kuɗaɗen har sau biyu a cikinsu.

“Waɗannan kwangiloli ne da aka yi tun shekarar 2018, sannan wasu mutane masu karfin hali suka fito da suka bayyana batun.

Ya ce an buga takardun bogi a cikin ma’aikatun, sannan da haɗin-bakin wasu ma’aikata, aka kirkiri takardun karya tare da biyan kuɗi.

Bawa ya ce muddin aka mayar da harkoin gwamnati ta hanyar zamani, ba za a samu irin waɗannan badaƙaloli ba.

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp