fidelitybank

Mu na cikin mawuyacin hali saboda ba albashi – Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Najeriya

Date:

Aƙalla ma’aikata 450 ne da ke aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashe 109 ba su samu albashinsu ba na wata biyar zuwa shida.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ma’aikatan da ke ƙarƙashin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya na cikin mawuyacin hali na rashin kuɗi ta yadda wasunsu ba ko iya biyan kuɗin haya da kuɗin makarantar ‘ya’yansu ko biyan wasu muhimman buƙatun iyalinsu.

Mai riƙon muƙamin kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce ma’aikatar na sane da wannan hali da ma’aikatan ke ciki, ya kuma bayar da tabbacin cewa za a shawo kan matsalar.

Manyan jami’an fadar gwamnatin tarayya da kuma jami’an da ke aiki a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya sun bayyana wa jaridar cewa ana buƙatar dala biliyan ɗaya domin biyan bashi da kuma tafiyar da harkokin ofisoshin jakadancin ƙasar daban-daban a ƙasashen duniya.

A lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki ya sake nazarin manufofin waje na ƙasar inda ya dawo da jakadu 83 a watan Satumba na 2023.

Sai dai kuma matsalar rashin kuɗi ta haifar da jinkiri wajen naɗa sababbin jakadun har yanzu.

To amma jaridar ta ruwaito cewa rashjin naɗa jakadun ya ƙara haifar da jinkiri wajen biyan albashin ma’iakatan ofisoshin jakadancin na Najeriya.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp