Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas, ta yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike da ya koma jam’iyyar saboda a na bukatarsa.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Tony Okocha, ya ce jam’iyyar ce ke kan mulki, don haka ya kamata Wike ya shiga.
Ya zanta da manema labarai a Fatakwal bayan ‘yan majalisar jihar 27 sun koma APC.
Da aka tambaye shi ko sauya shekar wani bangare ne na shirin Wike ya koma APC, Okocha ya ce: “Bana tunanin haka.
“Ko menene dalilinsu idan sun isa gadar za su tsallaka ta.
‘’Wike dan siyasa ne da sunansa ya girgiza a cikin al’umma; don haka babu wanda zai iya tunani ko ya ce masa idan zai koma APC ko a’a.
“A 2023, ya taimaka kwarai da gaske wajen nasarar APC a jihar.
“Mafi kyawun abin da muke rokonsa ya yi shi ne ya zo ya koma jam’iyyar APC domin ita ce ke mulki.”