fidelitybank

Mu na bukatar dala miliyan 910 don tallafawa Najeriya – UNICEF

Date:

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tana buƙatar dala miliyan 910 domin shawo kan matsalar jin ƙai a arewa maso gabashin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan rahoton haɗin guiwa da gwamnatin tarayya da majalisar dinkin duniya suka fitar a watan Nuwanba na 2024 wanda ya nuna cewa ƙasar na fuskantar matsalar yunwa, inda mutane sama da miliyan 30 aka yi hasashen cewa za su fuskanci ƙarancin abinci a 2025.

A wajen taron ƙaddamar da kundun tsare-tsaren ayyukan jin ƙai na arewa maso gabas da ya gudana a jiya Alhamis a Abuja, MDD ta jaddada cewa “Mutane kusan miliyan takwas na buƙatar agaji a jihohin, Borno da Adamawa da Yobe, inda ke akwai mutane miliyan 2.3 da suka rasa muhallansu.

MDD ta ce rikicin da ake fuskanta a ƙasashen Ukraine da Gaza da Sudan ne suka dauke hankalin duniya daga na arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar takardun Majalisar Dinkin Duniya, bukatar kudi da ake da ita a yanzu ya sanya matsalar jin ƙai a arewa maso gabas ta zama mafi tsada a yammaci da tsakiyar Afirka; kuma mai yiwuwa ya zarce na Chadi, Mali, Burkina Faso, da Nijar. In ji BBC.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp