Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce hukumomi na bakin kokarinsu wajen ganin sun ceto sauran ɗalibai da ƴan bindiga suka sace daga jami’ar tarayya ta Gusau.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, sa’ilin da ya kai ziyara a harabar jami’ar da ke Gusau.
A lokacin ziyarar, gwamnan ya kuma sha alwashin ganin an samar da tsaro yadda ya kamata domin a ci gaba da tafiyar da lamurra yadda suka kamata.
Kusan mako biyu ke nan bayan da wasu ƴan bindiga suka kai hari a unguwar Sabon Gida da ke maƙwaftaka da jami’ar, inda suka yi awon-gaba da ɗalibai sama da 20.
Daga baya hukumomi sun tabbatar da cewa an samu nasarar karɓo ɗalibai 14 da wasu ma’aikata biyu.
Sai dai har yanzu sauarn mutanen na a hannun ƴan bidiga.