Ukraine ta ce ita ta kai hari yau Juma’a a Tekun Bahar Aswad da ke yankin Crimea.
Sojojin Ukraine ɗin sun ce harin na makami mai linzami ya lalata sansanin soji a birnin Sevastopol.
Wata majiya a rundunar sojin saman Ukraine ta shaida wa BBC cewa Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami da ƙasashen yamma suka ba ta wajen kai harin a Crimea.
A makon da ya gabata ma sun kai wani hari a sansanin soji da ke Crimea wanda ya lalata wani jirgin ruwa na Rasha.