Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce su suka hana a cire tallafin mai a lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, lokacin da ake shirin cire tallafin.
A wata hira da BBC Sanatan ya ce a lokacin da yake shugabancin majalisar, lokacin da ake yunƙurin cire tallafin ne, ya je wajen Shugaba Buhari ya gana da shi a kan batun, inda daga nan ne shugaban ya ce masa shi ba bai gaya wa kowa a cire tallafin ba.
Sanatan ya ce sakamakon kafewa da suka yi da wannan ganawa da ya yi da Buhari shi ne ba a cire tallafin a lokacin ba.
”Haka kuma mun ki yarda a ƙara kuɗin wutar lantarki a lokacin ma,” in ji Sanatan.
Ahmad yana mayar da martani ne kan yadda ake cewa ƴan majalisun dokoki na zama ƴan-amshin-shata ga ɓangaren zartarwa na gwamnati.
”In ka ji mutum yana ƴan-amshin-shata, irin mutanen nan ne masu samun dama a ba su rediyo su je gidan talabijin wanda ba su da kowa su yi ta magana na soki-burutsu na shiririta,” in ji shi.