fidelitybank

Mu da Ten Hag kamar tif da taya ne – Mc Tominay

Date:

Scott McTominay ya ce, suna goyon bayan Erik ten Hag kan yadda yake gudanar da aikinsa, bayan kalubale da Manchester United ke fuskanta a bana.

Ranar Asabar ne Bournemouth ta doke United 3-0 a Old Trafford yayin karawar Premier League karo na 11 daga wasa 23 da ta yi rashin nasara a dukkan wasannin da ta buga kenan.

Ya zama wajibi United ta doke Bayern Munich, idan tana son kai wa zagaye na biyu a Champions League a kakar nan.

Bayern Munich, wadda ta kai zagaye na biyu a gasar zakarun Turai za ta ziyarci Man United mai maki hudu ta karshen teburi ranar Talata.

”Hakki ne na dukkan ‘yan wasa, shi ne kan gaba kuma mafi muhimmanci,” in ji McTominay.

”Muna da fitattun ‘yan wasa, yanzu haka muna kara kaimi don ganin mun koma kan ganiya.”

”Muna da kwararrren koci da masu taimaka masa. Muna so mu mayar da kungiyarmu kan ganiya. Wannann shi ne fatanmu.”

McTominay, mai shekara 27, ya fara buga wa Manchester United wasa a 2017 karkashin Jose Mourinho.

A makon jiya ne Ten Hag, wanda yake kakarsa ta biyu a Old Trafford, ya yi watsi da cewar rabin ‘yan wasan United ba sa tare da shi, ya ce dukkan ‘yan kwallon kansu a hade yake.

Wasu tsoffin koci-kocin United, David Moyes da Louis van Gaal da Mourinho da Ole Gunnar Solskjaer da kuma Ralf Rangnick, sun samu kansu cikin matsalar rashin jituwa da ‘yan wasa.

United tana mataki na shida a teburin Premier League kuma ta karshe a teburin Champions League, wadda ke bukatar doke Bayern Munich kafin ta kai zagayen ‘yan 16.

www.legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp