Wani tsohon ɗan majalisar wakilai, Dachung Bagos ya bayyana cewa wasu mutanen da marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa, sun ci amanar yardar da ya yi musu.
Ya ce lamarin ya janyo taɓarɓarewar batun cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa.
Bagos ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa na Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Talata, jim kaɗan bayan binne tsohon shugaban a garin mahaifarsa ta Daura.
“Buhari ya naɗa mutane ne da ya yarda da su waɗanda kuma yake tsammanin za su taimaka mi shi lokacin mulki, amma suka ci amanarsa daga baya.
“Buhari mutumin kirki ne kuma dattijo mai nagarta mai yaƙi da rashawa da son tabbatar da gaskiya – sai dai ba haka mutanen da ya naɗa suke ba, inda a yau za ka ga wasu da aka naɗa lokacin mulkinsa suna fama da shari’a kan zargin cin hanci,” in ji tsohon ɗan majalisar wakilan.