fidelitybank

Mtasalar tsaro na kokarin kawo cikas a zaben 2023 – Kungiyar Kare Hakki

Date:

Ƙungiyar da ke hanƙoron tabbatar da ƴancin bil’adama ta Human Rights Watch, ta ce, rashin hukunta waɗanda aka kama da laifi a zaɓukan ƙasar na baya da kuma gazawar gwamnati na magance matsalar tsaro na barazana ga aiwatar da babban zaɓen ƙasar na 2023.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne al’ummar Najeriya za su zaɓi sabon shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa’adin shugabancinsa, tare da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, bayan mako biyu kuma za su fita domin kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi.

An dai yi ta samun barazanar tsaro game da zaɓen daga ƙungiyoyi daban-daban a faɗin ƙasar, ciki har da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke yunƙurin daƙile yiyuwar zaɓen.

Karanta Wannan: Gwamnati ki kare ‘yan Jarida a zaben 2023 – CJID

Tarihin zaɓukan Najeriya ya nuna yadda zaɓukan ke cike da rigingimu da sauran laifukan zaɓe.

Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta ce zaɓen Najeriya na 2015 wanda ya bai wa shugaba mai ci Muhammadu Buhari nasara a matsayin ɗan takarar jam’iyyar adawa na farko da ya yi nasara zaɓen ƙasar shi ne ake gani wanda aka yi cikin kwanciyar hankali.

To amma an samu ‘yar hatsaniya a zaɓen 2019, ciki har da amfani da jami’an tsaro wajen yin barazana ga masu kaɗa ƙuri’a da kuma ‘yan dabar siyasa da ke yi wa ‘yan siyasa aiki.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...

Lauyan Sowore ya bukaci a sake shi cikin gaggawa

Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele...

Najeriya da Indiya za su haɗa kai na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Jihohi 19 da za a yi kwana 9 a na ruwan sama harda Kano – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen za a shafe kwana...

Tinubu ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar matar MKO Abiola

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa...

Abubuwan da Kwamiti ya gano a wajen Kwamishina mai murabus na Kano

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu,...
X whatsapp