Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ce, Sanata Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa a jamâiyyar APC, yana da rai kuma ba ya bukatar ya nuna wa kowa wata hujja ta rayuwa.
Ya bayyana haka ne a safiyar yau yayin da yake gabatar da tambayoyi a Channels TV.
Ku tuna cewa an yi ta rade-radin cewa, dan takarar jamâiyyar APC na iya fuskantar wasu matsalolin rashin lafiya biyo bayan rashin halartar wata yarjejeniyar zaman lafiya da âyan takarar shugaban kasa na jamâiyyun siyasa suka yi.
Rahotanni sun bayyana a ranar Alhamis cewa a halin yanzu yana birnin Landan na kasar Birtaniya.
Duk da haka, Tinubu ya kuma raba bidiyo na kansa yana aiki a kan keken motsa jiki don tabbatar da cewa yana da karfi da lafiya.
Sai dai ya kasa bayyana dalilin da ya sa ba ya nan.
Da yake mayar da martani kan jita-jitar, Gwamna Umahi ya bayyana cewa mutanen da ke tambaya game da lafiyar shugabannin kasar, ciki har da na dan takarar jamâiyyarsa, na yin kadan.
âBabu wanda ke da lafiya kwata-kwata, kuma ba wanda ke rashin lafiya kwata-kwata; wannan batu daya ne. Wani batu kuma shi ne, âyan Nijeriya qanana ne; wasun mu kanana ne.
âMutumin da ke motsa jiki, kun san ana yin bidiyo da yawo a kafafen sada zumunta ba tare da saninsa ba.
âSaboda haka, mutumin da ke da rai baya buĈatar nuna wata hujja ta rayuwa. Asiwaju yana da rai, kuma baya buĈatar nuna wata hujja ta rayuwa, kuma kuna iya ganin hakan.
“Ina ganin ya kamata mu mai da hankali kan abubuwan da za a iya gani saboda rayuwa kamar kasancewa cikin bas ne, kuma ba ku san inda tashar bas ta gaba take ba.
âWasu daga cikin mutanen da ke magana kan lafiyar shugabannin kasar ba su ma san lokacin da tashar motar su ta zo ba. Don haka, ya kamata mu dogara ga abubuwan zahiri. Kowane rai da lafiya yana hannun Allah; haka nake kallo”, in ji shi.