Gwamnatin tarayya ta ce, manyan motoci 31 aka tanadar domin kwaso ‘yan ƙasar da suka maƙale a Sudan, don kai su Masar inda za a ɗauko su a jiragen sama zuwa Najeriya.
Babban sakatare a ma’aikatar jin-kai ta ƙasar, kuma shugaban cibiyar da ke sa ido kan halin da ‘yan ƙasar ke ciki a Sudan Dakta Nasir Sani Gwarzo ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan wata ganawar sirri da manyan jami’an ma’aikatar a Abuja.
Ya ce an samar da manyan motocin ɗaukar fasinja 31, domin aikin kwasar ‘yar ƙasar da suka maƙale a Sudan ɗin, kuma an biya kowacce mota dala 30,000.
Ya ce jinkirin da aka samu a kan iyakar ƙasar Masar, an same shi sakamakon rashin biyan kuɗin da babban bankin ƙasar ya yi a kan lokaci, tare da buƙatar biyan kuɗin bisa da gwamnatin Masar ta yi.
Dakta Nasir Gwarzo ya ce, masu motocin sun buƙaci a biya su kuɗinsu gaba-ɗaya, duk kuwa da suna sane da cewa ba zai yiwu a tura kuɗi kai tsaye zuwa Sudan ba, dole sai da wakilai.
Ya ƙara da cewa ma’aikatar na aiki ne da hukumar tsaron farin kaya ta ƙasar da hukumar da ke tattara bayanan sirri a kan laifukan da suka shafi kuɗi ta Najeriya, wato Nigeria Financial Intelligence Unit (NFIU) wajen biyan kuɗaɗen.