Mota ta kade wani mutum ya mutu a lokacin da yake taimaka wa wasu agwagi tsallaka titi a garin Rocklin na jihar Californa ta Amurka kamar yadda ƴan sanda suka tabbatar.
Casey Rivara, mai shekara 41, ya fita daga motarsa ne ya je ya taimaka wa wani jerin gwanon agwagi tsallaka titi, sai wani matashi dan shekara goma sha da ke tuka wata mota ya kade shi, a Rocklin, da ke nisan kilomita kusan 40 a arewa maso gabashin Sacramento, in ji ƴan sandan.
Bayanin ya nuna cewa kafin motar ta kade shi sai da mutumin ya tabbatar da agwagin sun tsallake titin, daga nan ne kuma sai tsautsayi ya fada masa motar ta kade shi.
Zuwa yanzu ba wanda aka kama dangane da hadarin wanda ya faru a ranar Alhamis da daddare da misalin karfe takwas da rabi na dare agogon kasar.
Hukumar ƴan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma ba lalle ba ne a tuhumi matashin da wani babban laifi ba.