Shahararren dan wasan kasar Brazil, Ronaldo Nazario, ya ce, ya na son Morocco ta lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA a Qatar a shekarar 2022 a bana.
Ronaldo ya ce, Morocco na da hadin kai, ya kara da cewa ya na son yadda Atlas Lions ke kai hari da kuma kare su.
A cewarsa, yana tallafawa ‘yan Arewacin Afirka a gasar cin kofin duniya ta 2022.
Da yake magana da La Gazzetta dello Sport, Ronaldo ya ce, “Ina son su (Morocco) su lashe gasar cin kofin duniya. Komai yana da ban mamaki, yadda suke kai hari, yadda suke kare, yadda suke haɗin kai.
“Kuma ina sha’awar farin cikin da suka baiwa jama’arsu da kuma dukkanin Afirka, abin farin ciki ne da kwallon kafa kadai ke iya bayarwa.”
Morocco za ta fafata da Faransa a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya a daren Laraba.
Tawagar Walid Regragui ta kai wasan ne bayan ta kawar da Portugal a gasar cin kofin duniya a wasan kusa dana karshe.