Hukumomi a kasar Morocco sun yanke shawarar bibiyar dukkan tsofaffin rijiyoyin da ba a amfani da su a daukacin kasar, tun bayan mutuwar wani yaro da ya faɗa rijiya a lokacin da mahaifinsa ke aikin rijiyar.
An kwashe kwanaki a na kokarin kubutar da Rayan wanda ya fada rijiya mai zurfin mita 32, amma sai gawarsa aka ceto, abin da ya janyo tashin hankali a ciki da wajen ƙasar.
Wani jami’i a ma’aikatar ruwan kasar, Abdelaziz Zerouali, ya ce matakin duba tsofaffin rijiyoyin an dauke shi ne domin kauce wa faruwar hakan nan gaba.
Ya kara da cewa, a kowacce shekara ana hukunta dubban ‘yan Morocco da ke hakar rijiya ba bisa ka’ida ba, amma duk da haka lamarin ba ya sauki.