A karon farko Morocco ta kai wasan daf da na kusa da na karshe, bayan da ta yi nasara a kan Sifaniya a bugun fenariti a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.
Tawagogin biyu sun buga minti 90 ba ci daga nan aka yi karin minti 30, sannan aka kai minti 120 ba ci aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Abdelhamid Sabiri ya fara ci wa Morocco kwallo, sai Sifaniya ta barar da daya ta hannun Pablo Sarabia.
Hakim Ziyech na Morocco ya kara na biyu, sai Carlos Sole daga Sifaniya ya kasa cin wadda ya buga.
Sai dai kuma Badr Benoun ya kasa ci wa Morocco ta uku, kenan tawagar Afirka ta ci biyu kenan.
Sifaniya ta buga ta uku ta hannun kyaftin, Sergio Busquet, amma Bono ya tare, wanda ya hana ta Sole shiga raga.
Achrat Hakimi ne ya buga na uku ya kuma zura a raga, inda Morocco ta kai zagayen gaba da ci 3-0.
Morocco za ta kara da duk wadda ta yi nasara tsakanin Portugal da Switzerland ranar Asabar a fafatawar Quarter finals.