Ƙasar Maroko ta yi wa jakadanta da ke Sweden kiranye bayan wani gangami da aka yi na ƙona littafi mai tsarki na Al-ƙur’ani a birnin Stockholm na ƙasar Sweden.
Ma’aikatar harkokin wajen Maroko ta bayyana gangamin a matsayin cin fuska da kuma rashin hankali a lokacin da al’ummar Musulmin duniya ke bikin babbar Sallah.
Yanzu haka ana gudanar da bincike kan mutumin da ya assasa gangamin, Salwan Momik, wanda ɗan asalin ƙasar Iraqi ne.
Ana dai zargin sa da ƙoƙarin tayar da husuma da kuma rura wutar ƙiyayya.
Wata kotu a ƙasar Sweden ne ta tabbatar da ƴancin yin zanga-zangar da sunan ƴancin faɗin albarkacin baki.