Antonio Mohamed, kocin club UNAM ta Argentina, ya caccaki kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain akan sabon salon da suka dauka akan dan wasan gaba Lionel Messi.
Mohamed ya kira PSG a matsayin ‘mutane masu ɗaci,’ ya kara da cewa ‘yan Parisiya ba za su taba cin komai ba.
Hakan na zuwa ne bayan da PSG ta dakatar da Messi na tsawon makwanni biyu saboda balaguron da ya yi a Saudiyya ba tare da izini ba kwanakin baya.
Da yake magana da Ole (ta hanyar Bolavip), Mohamed ya yi imanin cewa PSG ta nuna rashin girmamawa ga Messi.
“Rashin girmamawa ne (ga Lionel Messi),” in ji Mohamed.
“Wadannan mutane masu ɗaci, waɗanda ba su taɓa cin wani abu ba, ba za su yi nasara ba ko da sun sayi Hasumiyar Eiffel suka sanya ta a gaban baka. Rashin girmamawa ne gaba ɗaya.”
Messi ya zura kwallaye 20 kuma ya taimaka 19 a wasanni 37 da ya buga a PSG a kakar wasa ta bana.