Terem Moffi yana cikin fafatawa a gasar Ligue 1 na watan Satumba.
Dan wasan zai fafata da abokin wasansa na OGC Nice Marcin Bulkan da kuma Marco Bizot na Brest domin samun kyautar.
‘Yan wasan Bulkan da Bizot ne masu tsaron gida.
Moffi ya taka rawar gani sosai ga Nice a cikin watan, inda ya yi rajistar kwallaye uku da taimakawa daya a wasanni uku na gasar Les Aiglons.
Dan wasan mai shekaru 23 a hankali yana samun kafarsa a gasar ta Faransa bayan da ya yi harbin kan mai uwa da wabi a wasannin farko na bana.
John Utaka, Vincent Enyeama da kuma Victor Osimhen su ne sauran ‘yan Najeriya da suka lashe kyautar a baya.